Cikekken bayani akan Yadda Ake Samun Kudi Ta Hanyar Blog ko Website Dama Yadda Ake Budewa


 Takai Ceccen Bayani Akan Website da kuma Yadda ake bude website.

Abu Na farko de shine, mai nene website?
Website shine hadakar shafika(Pages) wuri daya a yaanar gizo (Internet). Wadan nan shafika zaa su iya kasancewa rubutune aciki ko phatuna ne aciki kuma ma bidiyo ne aciki, ko ma Wanne ne aciki de Sunan sa web page ma'ana shafin internet, Toh hadaakar wadan nan web page din su ake cewa wuri daya shi ake cewa website.

Toh yaya ake Kir kiran website?
Abaya de, Kafin kimiya da fasaha su bun kasa Sossai yadda ake Kir kiran website shine ta hanyar "Coding" ko muce "Programming language" toh shi wannan programming language yare ne da ake koyan shi shima kamar turanci yake, idan mutum Ya kiyi wannan yare, sai mutum naimo wani abu da ake cewa "Text Editor" yarubuta duk irin abinda yake so a wannan Text Editor da wannan yaren na Programming language da ya koya. Bayan haka sai mutum ya sake Wani abu da ake cewa "Interpreter" Ita kuma interpreter sai ta fassara wannan Programming language zuwa Machine language, Shi kuma machine language shine yaren da computer ta keji, Yadda yaren yake shine 0s da 1s (010101010100101011010) wannan yaren kawai computer ta sani.
Daga cikin Programming language din HTML, CSS, JavaScript da PHP da de Sauransu.

Toh ana nan duniya tana kara ciga ana samun sauki, sai aka samu wani manhaja(Software) da ake ce da ita "Web development tool" misalin wannan manhaja sune kamar su Dreamweaver, Wannan manhaja tana sauka kawa duk wani mai kir kiran website ya Kir kiri website batare da Ya iya Coding ba ko Programming language ba.

Har ila yau de ana samun cigaba aka samu wata manhaja da ake cewa "wordpress" its wannan manhaja ta wordpress ita kuma design website din kawai mutum dubawa zai yi Ya zabi wanda yamasa yayi installing Akan Web Hosting, Bayani akan web Hosting Yana nan tafe bada jumawa ba insha Allah.

Haka zalika aka sake samun itama wata manhaja da ake ce da ita "Blogger" Ita wannan manhaja ta Blogger kamfanin Google ne su kirkiro ta, ita ma zatabawa mutum dama yayi installing din Template Design din da mutum yake so ko kuma mutum yayi amfani da Theme din blogger, Da din shine Ba sai mutum yasayi Web Hosting ba, Shi kyauta, Dan haka Gani ko koyan Yadda Ake bude website da Blogger Kalli bidiyon da ke kasa


Sauran Banai Kuma Suna Cikin Darusan Mu Na Video Dake YouTube Channel Na